An kai karar karbo kudaden da Madoff ya sata

Bernard Madoff
Image caption Mutumin da ya fi kowa damfara

Kwamitin amintattun da Amurka ta kafa kan gano kudade mafi yawa da aka taba sacewa a tarihin zambar kudi a duniya, ya shigar da wasu kararrakin neman karbo kimanin dala biliyan ashirin.

Yayin da wa'adin ikirarin gano kudaden da aka sace wadanda suka fi yawa a tarihin zambar kudi a duniya ya rage saura yan sa'o'i kalilan, kwamitin amintattun da kotun Amurka ta kafa ya shigar da karar neman maido kudi kimanin dala biliyan ashirin.

Wadannan kudade na daga cikin dala biliyan sittin da biyar da ake zargin attajirin nan na New York Bernard Madoff, wanda yanzu haka ya ke gidan yari a Amurka, ya yi awon gaba da su.

Wadannan jerin kararraki na zuwa ne daidai lokacin da wa'adin da aka bai wa kwamitin na shigar da kara ya rage sa'o'i kalilan ya cika.

Masu gabatar da karar dai na zargin wata ma'aikaciyar banki a Austria Sonja Kohn da taimakawa Mr Madoff.

Sai dai lauyanta ya musanta wannan zargi, inda ya ce ita ma ta na cikin wadanda Madoff ya damfara.