Amurka zata yiwa dukkanin jiragen samanta rajista

Jirgin saman Amurka
Image caption Gwamnatin Amurka zata yiwa dukkanin jiragen kasar rajista a shekara mai zuwa

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta rasa bayanai game da wasu dubban jiragen sama dake kasar wadanda ake jigila dasu.

Ma'aikatar dake kula da zirga zirgar jiragen sama ta kasar ta ce daga shekara mai zuwa, tilas a sake yiwa kowanne jirgin sama dake kasar rajista don tabbatar da adadin jiragen sama da ake zirga zirga dasu a kasar.

Wakilin BBC ya ce akwai fiye da jiragen sama dubu dari uku da hamsin dake hannun wasu mutane masu zaman kansu da kuma 'yan kasuwa a Amurka, kuma

Daya bisa uku na jiragen, hukumar ta ce tana da shakku game da bayanansu, saboda bacewar wasu takardu da kuma wasu matsaloli daban daban.