An hallaka mutane 3 a wata zanga zanga a Bangladesh

Bangladesh
Image caption Bangladesh

Rikici ya barke a kasar Bangladesh tsakanin jami'an tsaro da ma'ikatan dinka tufafi akan bukatar aiwatar da albashi mafi karanci, wanda ya kamata a fara aiwatarwa tun watan da ya gabata.

Jami'an 'yan sanda a kudancin birnin Chittagong sun ce akalla mutane uku sun rasu sannan da dama sun jikkata.

Tuni wani kamfani Koriya ta Kudu ya rufe rassan kamfaninsa guda goma sha daya a ranar asabar saboda takaddamar.

'Yan sanda a Dhaka, babban birnin kasar sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa dubban ma'aikata masu zanga-zanga saboda rufe ma'aikatun nasu.

An toshe hanyoyi tare da cinnawa motoci wuta a birnin na Dhaka.