Zaben CPC a Kano ya bar baya da kura

Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC
Image caption Wasu 'ya'yan jam'iyyar CPC a jahar Kano sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin gamsuwarsu game da yadda suka ce jam'iyyar ta gudanar da zabukanta na cikin gida

A jihar Kano dake arewacin Najeriya, zabukan da jam'iyyar adawa ta CPC ta gudanar na cikin gida ya haifar da kace- nace tsakanin 'ya'yan jam'iyyar a jihar, inda wasu ke zargin ba'a yi zabubbukan a mafi yawan mazabun jihar ba.

Wasu 'ya'yan jam'iyyar da dama sun bayyana cewa har ya zuwa yammacin jiya basu ga jami'an jam'iyyar da zasu gudanar da zabukan ba.

Hakan tasa wasu matasan jam'iyyar suka gudanar da wata zanga zangar lumana a birnin na Kano don nuna rashin gamsuwa da abinda suka ce take-taken almundahana a zabubbukan.

Su dai masu wannan korafi suna zargin shugabannin jam'iyyar a jahar da yin amfani da zabukan don kokarin sharewa wani dan takara hanya, cikin mutane takwas dake neman jam'iyyar ta tsaida su takarar gwamna.

To amma shugaban jam'iyyar CPC a jahar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya musanta zarge zargen, inda yace an gudanar da zabukan cikin adalci.