Rikicin siyasar kasar Ivory Coast

Zababben shugaban IvoryCoast Alassane Ouattara
Image caption Mr. Alassane Ouattara ya nemi shugaba Laurent Gbagbo ya mika mashi mulkin kasar kafin a fara duk wata tattaunawa.

Mutumin da kasashen duniya suka sani a matsayin wanda ya lashen zaben shugaban kasar Ivory Coast da ake takaddama akai, ya ce tilas sai shugaban dake kan karagar mulki a yanzu Laurent Gbagbo, ya mika mulki kafin bangarorin biyu su fara tattaunawa.

Kakakin Mr. Alassane Wattara, Patrick Achi, ya ce ba suna adawa da tattaunawa bane, sai dai tilas a amince da cewa Alassane Wattara, shine zababben shugaban kasar, idan ba haka ba kuma, babu wata tattaunawa da zasu shiga.

Kungiyar tarayyar Afrika dai ta dakatar da kasar ta Ivory Coast daga cikinta matukar Laurent Gbagbo zai ci gaba da rike madafun iko.