'Yan Sanda sun fara binciken fashewar bamb a Sweden

Fashewar Bomb a Sweden

Jami'an 'yan sanda na kasar Sweden sun ce suna gudanar da bincike akan abun nan da ya fashe a Stockholm babban birnin kasar, kuma sun dauki al'amarina matsayin wani aikin ta'addanci.

Firaministan kasar Fredrik Reinfeldt yayi tir da wadannan hare-hare sannan yace ba za a amince da su ba a kasa dake bin tafarkin dimukuradiyya.

Mutane biyu ne suka samu raunika, yayin da wani kuma ya mutu a sakamakon fashewar abun.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sweden yace 'yan minitina kadan gabanin fashewar bama-baman, jami'an tsaro sun sami wani sako na email dake yin barazanar kai harin, saboda kasar Sweden bata yir tir da batancin da aka yi wa Annabi Muhammad (SAW) ba.

Haka nan kuma sakon na email ya yi tsokaci da kasancewar sojojin Sweden a Afghanistan.