Gwamna Jang na son halaka mu, in ji 'yan majalisar Filato

Gwamnan Filato, Jonah Jang
Image caption 'Yan majalisa sun zargi Jang da yunkurin halaka su

Wasu 'yan majalisar dokokin jihar Filato, da ke Najeriya na zargin gwamnan jihar Jonah Jang da kulla makarkashiyar hallakasu tun bayan da suka yi yunkurin tsigeshi daga kan kujerarsa.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Ibrahim Baba Hassan ne ya yi wannan zargi, inda ya ce sau uku jami'an gwamnati na tura matasa majalisar domin hana ta zama tare da kurarin halaka su.

Kan haka ne 'yan majalisar ke neman gwamnatin tarayya da sauran hukumomin tsaro da su kai dauki jihar.

Sai dai a nasu bangaren, mukarraban gwamnan sun musanta wannan zargi inda suka ce kullum kokarinsu shi ne tabbatar da zaman lafiya a jihar ta Filato mai fama da rikici.