Kotu ta ce a tasa keyar Ibori zuwa Burtaniya

Image caption Tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori

Wata babbar kotu a kasar Dubai, ta ba da umarnin a mika tsohon gwamnan jihar Delta dake Kudu maso Kudancin Najeriya James Ibori, ga mahukuntan Burtaniya domin ya fuskanci shari'a.

Kotun ta ce babu wani dalili da zai sa ta dakatar da yunkurin da ake yi na gurfanar da mista Ibori a gaban shari'a.

Ana dai zargin Mista Ibori ne da laifin halarta kudaden haram tare da sace kudaden gwamnatin jihar ta Delta lokacin da yake kan karagar mulki.

Masu bincike a Burtaniya sun zargi Mista Ibori da sama da fadi da kusan dala miliyan dari uku na kudin jihar shi a lokacin da ya ke kan kujerar gwamna.

Kotu ta bada dalili

Kotun ta ce tun da dai laifin da ake zargin Mista Ibori da aikatawa na halartar kudaden haram ne, to babu dalilin da zai sa ta hana tasa keyarsa zuwa Burtaniya domin fuskantar shari'a.

Masu gabatar da kara a Burtaniya da kuma Najeriya na zargin Mr Ibori da sace kudaden da yawansu su kai dala miliyan 290, inda ake kyautata zaton an karkatar da su ne ta hanyar wasu bankunan Burtaniya.

Abin da yasa jami'an Burtaniya dana Najeriyar ke son yi masa shari'a bisa zargin cin hanci da rashawa, zargin da kuma ya musanta.

To ko yaya hukumar EFCC mai yaki yiwa tatalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya ta ji da hukuncin, mai magana da yawunta Mista Femi Babafemi ya shaidawa BBC cewa: "Wannan hukuncin da kotun daukaka kara ta Dubai ta yanke ya tabbatar da abinda muke fada wanda kuma kotun farko ta tabbatar.Kuma ya nuna cewa akwai adalci a ko'ina cikin duniya."

To ko wannan na nufin Najeriya za ta nemi mahukunta a Burtaniya su mika mata James Ibori domin tai masa shari'a sai ya ce;

"A yanzu muna aiki tare da mahukuntan Burtaniya, daga baya kuma ya mu dauki matakin da ya dace, amma yanzu ba zam fadi a bin da muke shirin yi ba."

An daure na kusa da Ibori

A shekara ta 2007, wata kotu a Burtaniya ta kwace wasu kadarori da ake zargin na sa ne, wadanda su ka tasamma dala miliyan 35. Albashin sa dai a wata bai kai dala dubu 25 ba.

Image caption Theresa Ibori, tsohuwar matar James Ibori

Tuni dai kotu a London ta samu Theresa Ibori tsohuwar matar James Ibori da laifi, sanan ta daure ta shekaru biyar a gidan yari.

Baya ga ita, an kuma sami 'yar uwarsa Christine Ibori-Ibie da farkarsa Udoamaka Onuigbo, da laifin tallafa masa wajen halarta kudin haram, sannan aka daure su na tsawon shekaru biyar.

An fara kama mista Ibnori ne a Najeriya a shekara ta 2007. Amma bayan shekarau 2 sai wata kotu a Asaba ta wanke shi daga zargi 170 din da aka yi masa.

Babbu dai tabbas ko sai yaushe ne za a mika mista Ibori zuwa kasar ta Burtaniya.

A watan Mayu ne aka kama shi a kasar ta Dubai, karkashin sammacin kungiyar 'yan sandan kasa da kasa.

Wanann hukunci da kotun ta Dubai ta yanke ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan makomar mutanen da ke zargi da aikata laifukan da ke da alaka da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Bada lallai bane a ce wanann hukuncin zai kawo karshen ja'inja ta fusakar shari'a kan muista Ibroi, ganin cewa yana da damar daukaka kara zuwa kotu ta sama.

Najeriya, wacce ta fi kowacce kasa yawan jama'a a nahiyar Afrika, tana daya daga cikin kasashen da suka fi fama da cin hanci da rashawa a duniya.

Tsofaffin gwamnoni da dama ne wadanda suka yi aiki karkashin gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo aka kama, inda ake zarginsu da laifin sama da fadi da dukiyar jama'a.