An kori ministan harkokin wajen Iran

Manouchehr Mottaki
Image caption Manouchehr Mottaki

An kori ministan harkokin wajen Iran, Manouchehr Mottaki daga kan mukamin nasa.

An kore shi ne a daidai lokacin da yake ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka.

An sanar da matakin ne a cikin wata sanarwa daga shugaban Iran din, Mahmoud Ahmadinejad. To amma ba a bayyana dalili ba.

Wakilin BBC a birnin Tehran ya ce, korar Manouchehr Mottaki, wanda ya kwashe shekaru biyar a matsayin ministan harkokin wajen Iran din, ta zo da mamaki.

To amma kuma in ji shi, mai yiwuwa wata alama ce da ke nuni da irin gwagwarmayar ikon da ake a cikin jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya, wadda ke mulki a kasar.

Ana daukar Manouchehr Mottaki a matsayin na kurkusa da masu ra'ayin 'yan mazan jiyan da ke adawa da shugaba Ahmadinejad, a majalisar dokokin kasar.

A yanzu Ali Akbar Salehi, shugaban kwamitin makamashin nukiliyar Iran din, shine zai maye gurbin Manouchehr Mottakin.