Ma'aikatan NAFDAC na yajin aiki

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya ma'aikatan hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasar, NAFDAC suka tsunduma cikin yajin aiki na sai abin da hali yayi.

Ma'aikatan sun ce sun dauki matakin ne, saboda rashin ci gaba da biyan su hakkokinsu na sabon tsarin albashi.

Suna korafin cewa tuni sauran takwarorinsu a wasu ma'aikatun tarayyar suke amfana da sabon tsarin albashin, amma su har yanzu ba su ji wani takamaiman bayani daga gwamnati ba.

Masu yajin aikin sun koka da kuncin rayuwar da suka shiga, sakamakon rashin biyansu hakkokinsu.