Gwamnonin Arewa sun yi watsi da matakin majalisa

gwamnonin Arewa sun yi fatali da matakin majalisa
Image caption gwamnonin Arewa sun yi fatali da matakin majalisa

A Najeriya, kungiyar gwamnonin jihohin Arewacin kasar, ta bi sahun kungiyar gwamnonin jam`iyyar PDP mai mulkin kasar wajen yin Allah-wadai da wasu sauye-sauye da majalisar wakilan kasar ta yi wa dokokin zabe.

Gwamnonin dai sun yi zargin cewa sauye-sauyen, babu abinda zai haifar na amfani ga kasa, in banda baiwa yan majalisar damar mamaye harkokin siyasa a Najeriya.

Sanawar da kungiyar ta yi bayan zaman da ta yi a Abuja ta bayyana cewa sauye-sauyen ba alheri ba ne ga habakar demokuradiyya a Najeriya, kuma kungiyar za ta yi iya yinta wajen ganin hakar yan majalisar ba ta cimma ruwa.

Yan Majalisar Wakilan sun mai da martani a kan matsayin da gwamnonin jam'iyyar PDP, inda suka ce sun makaro don kuwa tuni ta riga ta amince da gyaran.