Jam'iyar PDP ta fusata gwamnoni

Tambarin jam'iyar PDP dake mulkin Najeriya
Image caption Jam'iyar PDP ta fusata gwamnoni

Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam`iyyar PDP dake Najeriya sun nuna rashin jin dadi kan sauyin da jam`iyyar ta yi ga yadda za ta gudanar da zaben-fidda-gwani na masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar a inuwarta.

Jam'iyar ta ce a yanzu za ta gudanar da zaben-fidda-gwanin ne a birnin tarayya Abuja, sabanin yadda aka tsara za a gudanar a matakin jiha-jiha a baya.

Sai dai hakan bai yiwa gwamnonin dadi ba, abin da suke gani wata hanya ce ta karya lagon da suke da shi a jam'iyar.

Alhaji Murtala Nyako, shi ne gwamnan jihar Adamawa, ya shaidawa BBC cewa:''Ina tsammanin ba mu kadai ne (bamu ji dadin abin da jam'iyar ta yi ba), kowa ma bai ji dadin tsarin ba.Har yanzu ta na-kasa-ta na-dabo''.