Kotu ta bayar da belin Julian Assange

Julian Assange a motar daukar masu laifi
Image caption Julian Assange a motar daukar masu laifi

Wata kotu a nan London ta bayar da belin , Julian Asange, shugaban shafin nan na intanet, Wikileaks, mai kwarmata bayanan sirrin da aka tsegunta masa, wanda ya harzuka gwamnatin Amurka,saboda wallafa wasu muhimman bayanan diplomasiya.

Sai dai Mr Assange din zai ci gaba da kasancewa a tsare, har zuwa lokacin da aka saurari karar da masu gabatar da kara na kasar Sweden suka daukaka, cikin kwanaki biyu.

Lauyan Mr Assange, Mark Stephens ya ce , "Mu masu kare shi ta fuskar shari'a, mun san cewa mutumin nan ba shi da laifin komi, amma za a kyale shi ya sake shafe wata ranar a dakin kurkuku, inda aka hana shi damar saduwa ko magana da sauran fursunoni".

Mr Assange dai na kalubalantar wani yunkuri ne na tasa keyarsa zuwa kasar ta Sweden domin fuskantar wasu laifukka masu nasaba da aikata fyade.