Berlusconi ya tsallake rijiya da baya

Berlusconi ya tsallake rijiya da baya
Image caption Silvio Berlusconi yana barin ginin Majalisar Dattawa bayan kada kuri'a

Fira ministan Italiya Silvio Berlusconi, zai ci gaba da rike ragamar ikon kasar, bayan samun nasara a zabuka biyu da aka gudanar a majalisar dokokin kasar.

Ya samu nasara ne da kuri'u uku kacal, bayan wani zama mai cike da hargisti da Majalisar wakilan kasar ta gudanar, hadi da zanga-zangar da jama'a suka gudanar a kan titunan birnin Rome.

Tun da farko mista Berlusconi ya samu nasara a makamanciyar wannan kuri'a da Majalisar Dattawa ta kada da gagarumin rinjaye.

Ya nemi 'yan Majalisar da ka da su kawo tsaiko ga daidaiton da tattalin arzikin kasar ke samu ta hanyar tsige shi.

Masu adawa da shi sun zarge shi da yin lako-lako wajen tafiyar da mulki, sannan kuma ana zarginsa da cin hanci da rashawa.

Mista Berlusconi, mai shekaru 74, ya ci rabin wa'adinsa na shekaru biyar, sai dai ya samu matsala saboda zargin da ake yi masa wanda ya hada da dangantakarsa da mata.

Sharhi

Wakilin BBC a birnin Rome Duncan Kennedy, ya ce wannan nasara na nufin cewa ya samu kansa a siyasance akalla zuwa sabuwar shekara.

Domin duk da cewa kamun kafar Mista Berlusconi da ya yi, ya kaishi ga gaci, zai ci gaba da fuskantar adawa anan gaba.

Dubban jama'a ne suka taru a birnin Rome da sauran manyan biranen Italiya domin neman sauyi a gwamnatin kasar.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye, sannan an ji karar fashewar da ake tunanin tarwasti ne na wuta.