CPC ta soke zaben cikin-gida

Janar Muhammadu Buhari dake son CPC ta tsayar da shi takara a zaben badi
Image caption An soke zaben cikin-gida na jam'iyar CPC

A ranar litinin ne kwamitin amintattun jam'iyyar CPC da ke Najeriya, ya soke zabukan cikin-gida da jam'iyar ta gudanar a jihohin Kano da Kebbi sakamakon magudin da kwamitin ya ce an tafka.

Haka kuma kwamitin ya rusa shugabancin jam'iyyar na jihohin Kano, da Kebbi, da Katsina, tare da nada kwamitocin rikon-kwarya da za su tafiyar da al'amuran jam'iyyar har zuwa kammala zabukan cikin-gida.

Injiniya Buba Galadima, wakili ne a kwamitin amintattun jam'iyyar, ya shaidawa BBC cewa sun soke zabukan cikin-gidan ne, sakamakon kin bin ka'ida da wadanda aka nada don gudanar da su suka yi.

Jam'iyar dai ta fada rikici bayan da wasu 'ya'yanta, musamman a jihar Kano suka yi korafin tafka magudi a zaben cikin-gidan da jam'iyar ta gudanar a jihar a karshen makon jiya.