Hukumar sojin Najeriya ta ce an kashe sojoji 8 a Neja Delta

Hukumomin Sojin Najeriya sun bada sanarwar mutuwar sojoji takwas a wani samame da su kai a sansanin wasu masu ikirarin kare yankin Niger Delta a garin Ayakoromo da ke Jihar Delta makwanni biyu da suka wuce.

Babban hafsan sojin kasa, Laftana Janar Onyeabo Azubike Ihejirika ne tabbatar da hakan a wani taro manema labarai a Abuja, inda ya kara da cewa fararen hula shidda ne suka mutu a lokacin harin da sojojin suka kai.

Sai dai al'umomin garin na Ayakoromo a jihar ta Delta sun zargi rundunar gamayyar tsaro ta JTF mai aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin ne da kashe masu mutane, a lokacin da sojojin ke artabu da dakarun Janar John Togo, wani mai adawa da shirin gwamnati na yin afuwa ga 'yan bindigar yankin na Niger Delta.

Al'umomin su zargi sojojin da bankawa kauyukansu wuta. To sai dai rundunar ta JTF ta ce akwai karin gishiri a ikirarin al'umar kauyen.