Man United ta dare saman tebur a Premier

Man United ta dare saman tebur a Premier
Image caption Ji-Sung Park ne ya zira kwallon da ta raba rigima

Kwallon da Ji-Sung Park ya zira ta bai wa Manchester United nasara da ci daya da nema a kan Arsenal, inda ta maye gurbinta a saman teburin Premier. Dan wasan na Koriya ta Kudu ya zira kwallon ne da ka bayanda Nani ya yo kurosin inda ta tsallake mai tsaron gida Wojciech Szczesny.

Wayne Rooney ya samu damar zira kwallo ta biyu, amma sai ya barar da bugun fanaretin da United ta samu bayanda Gael Clichy ya taba kwallon da hannu.

Dama mafi kyau da Arsenal ta samu ita ce ta Marouane Chamakh, amma sai dai bai samu nasarar zira kwallon ba.