Dan Najeriya ya zama dan Majalisa a Poland

Image caption Mista John Abraham Godson tare da magoya bayan sa

An rantsar da bakar fata na farko wanda dan Najeriya ne a matsayin dan Majalisar Dokoki a tarihin kasar Poland, kuma tuni har ya dare kan kujerarsa ta majalisar.

An haifi John Abraham Godson ne a Najeriya, a can kuma ya taso, amma kuma a yanzu dan kasar Poland ne.

Poland dai kasa ce ta galibi fararen fata, kuma mabiya darikar Roman Katolika.

Don haka ake yi wa zaben Mista Godson dan majalisar dokoki, da kuma zaben wani mutum na farko da ya fito fili ya amsa cewar shi dan luwadi ne a matsayin kansila a birnin Warsaw, a matsayin wani abin tarihi a harkokin siyasa da na zamantakewar kasar.

Bakar fata dubu hudu ne ke zama tsakanin jama'ar Poland miliyan talatin da takwas, kuma hankalin kafofin yada labarun kasar ya koma kan Mista Godson.

Lokocin da Mista Godson ya zo Poland

Tun a farkon shekarun 1990, Mista Godson ya fara zama a Poland inda ya fara aiki a matsayin malami, daga nan kuma ya koma aiki a wani cocin protestant a matsayin fada .

Mista Godson dai kansilla ne a garin Odz kuma ya karbi wanan kujerar ne bayan da wani abokin aikin sa daga jamiyyar masu sassaucin ra'ayi ya bar majalisar domin ya rike mukamin magajin garin na Odz.

Mista Godson dai na auren farar fata 'yar kasar Poland kuma 'ya'yan su hudu.

Sai dai Mr Godson ya ce a baya ya fusknaci matsalar wariyar launin fata; "Launin fatar ta kasance matsala.

"Da farko na rika shan duka, amma kuma sau biyu ne hakan ya faru, amma kuma a wasu lokutan za ka ji mutane na kiran ka da wasu irin sunaye ko kuma kalaman batanci, amma kuma an fara samun sauyi."

Sai dai duk da cewa wariyar launin fata kawo yanzu matsala ce a kasar, amma labarin Mista Godson ya nuna yadda ake samun sauyi a cikin al'ummar kasar Poland cikin sauri.