Richard Holbrooke ya mutu

Richard Holbrooke
Image caption Richard Holbrooke ya mutu

Daya daga cikin jami'an Difilomasiyyar da suka yi fice a Amurka, Richard Holbrooke ya mutu ya na da shekaru sittin da tara.

An dai fi sanin Mista Holbrooke ne, a kokarin da ya yi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta Daytona da ta kawo karshen yakin Bosnia a shekarar 1995.

Kazalika ya zama manzon musamman da shugaba Obama ya tura kasashen Afghanistan da Pakistan.

Mista Holbrooke, wanda dan jam'iyyar Democrat ne tsawon rayuwarsa,ya yi aiki na kut da kut da shugabannin Amurka na jam'iyyar Democrat guda uku, wato Carter da Clinton da Obama.

Tun ranar Juma'a dai aka kwantar da shi a asibiti a Washington bayan da ya fadi a wurin aiki.