Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da kudirin doka

Majalisar dattawan Najeriya
Image caption Majalisar dattawan Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da kudirin da ke kokarin baiwa 'yan majalisa damar zama mambobi a kwamitocin zartarwa na jam'iyyunsu.

A zaman da suka gudanar a yau, 'yan majalisar sun yi watsi da kudurin, wanda tuni 'yan majalisar wakilai suka amince da shi.

Kudurin dai ya fuskanci adawa daga bangarori da dama na kasar.

Tuni dai kungiyoyi dayawa, ciki har da gwamnonin kasar, suka yi Allah wadai da shirin. A yau wasu matasa dake zanga-zanga sun mamaye kofar shiga ginin Majalisar dokokin tarayya a Abuja, a daidai lokacin da 'yan majalisar dattawan ke tattaunawa a kan batun.