Makomar siyasar Berlusconi

Firaminstan Italiya, Silvio Berlusconi
Image caption Makomar siyasar Berlusconi

A yau ne majalisun dokokin kasar Italiya za su kada kuri'un yankan kauna kan Firaminista Silvio Berlusconi.

Ana hasashen za'a yi kankankan tsakanin 'yan adawa da magoya bayan Mr. Berlusconi a majalisar wakilai, kuma shan kayensa, na iya wajabta gudanar da sabon zabe a kasar.

Ranar litinin dai firaministan ya roki 'yan majalisun da su goya masa baya, inda ya ce a lokacin da duniya ke cikin rudani ta fuskar tattalin arziki, Italiya na bukatar dorewa ne kan tafarkin da ta ke bi, kuma raba shi da mulki rashin hankali ne.

Sai dai 'yan majalisar da suka fice daga kawancen jam'iyyun da ke mulkin kasar sun ce ba za su iya cigaba da zama da firaministan da abin kunya da kuma zarge-zargen cin rashawa suka dabaibayeshi ba.