An cirewa Tanja kariya daga tuhuma

Malam Mamadou Tanja
Image caption Malam Mamadou Tanja

Gwamnatin Nijar ta cire wa tsohon shugaban kasar, Malam Mamadou Tanja, rigar kariya daga tuhuma.

Kakakin gwamnatin kasar ne, Dokta Mahamane Laouali Dandah ya tabbatar wa BBC da matakin.

Dokta Dandah ya ce, a zaman da ta yi a ranar 15 ga wannan watan ne, kotun kasa, ko kuma Cour d'Etat, ta cire kariyar da tsohon shugaban ke da ita daga tuhuma.

A farkon watan Nuwamban da ya gabata, kotun kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, ta kasashen yammacin Afirka, ta umurci gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta saki tsohon shugaban.

ECOWAS ta ce, cigaba da tsare shi ba tare da an tuhume shi ba, ya sabawa dokokin kungiyar.

Tun lokacin da sojoji suka yi masa juyin mulki a watan Fabrairun da ya wuce, Malam Mamadou Tanja ke cigaba da zama a tsare.