Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce an samu nasarar yaki da malaria

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta jinjinawa abinda ta kira sakamako mafi faranta rai a yakinda ake yi da cutar malairia ko zazzabin cizon sauro cikin shekaru da dama.

Hukumar ta ce asarar rayukanda ake samu a kasashen Afirka da suka fi fama da cutar, ya ragu da kusan rabi a cikin shekaru gomanda suka gabata.

Babbar darektar hukumar lafiyar ta duniya -WHO, Margaret Chan ta ce, bayan shekaru da dama ana samun koma baya da tsaiko wurin yaki da cutar, a yanzu kasashen duniya da masu taimaka masu sun yunkuro.

Dabarun da ake amfani da su yanzu na aiki.

Sakamakon da aka samu cikin wannan rahoto, shine mafi faranta rai cikin shekaru da dama.