Dora ta ajiye aikin ta a yayinda ta koma APGA

Image caption Dora Akunyili

A Najeriya Ministar yadda labarai Ta kasar, Farfesa Dora Akunyili ta ajiye aikinta, a yayinda kuma ta fice daga jami'iyyar PDP, mai mulkin kasar.

Farfesa Akunyili wadda ta bada sanarwar komawa jami'iyyar adawa ta APGA ta ce za ta tsaya takarar neman kujerar Majalisar Dattijai ne a zabukan shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

Farfesa Akunyili ta ce za ta tsaya takarar kujerar majalisar dattijai ne karkashin jami'iyyar adawa ta APGA, saboda a cewar ta jamiyyar ta fi tasiri a jihar ta ta Anambra.

Akunyili ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na rueters cewa ta dau matakin komawa jam'iyyar APGA ne saboda irin gaggarumin ci gaba da aka samu a jihar Anambra wanda gwamna Peter Obi ya ke jagoranta karkashin jam'iyyar APGA.

Sauya sheka

Wannan dai ba sabon abu bane a siyasar Najeriya, ganin cewa 'yan siyasa da dama na sauya sheka domin neman bukatunsu.

Ana dai ganin ficewar Farfesa Akunyi daga jam'iyyar ta PDP na nuni da yadda jam'iyyar ke fuskantar matsaloli a yayinda ta ke shirin tunkurar zabukan shekara ta 2011.

A baya ma, kotu ta soke zabukan gwamnoni biyu karkashin inuwar jam'iyyar PDP a kudu maso yammacin kasar, inda ta mika kujerun ga jam'iyyar ACN.,Wannan dai na nufi cewa sannu a hankali jam'iyyar ta fara ja da baya a maimakon rinjayen da ta ke da shi a baya.

Jam'iyyar PDP dai ita ce har yanzu ke jagorancin kasar tun da aka koma bin tafarki demoradiyya a shekara ta 1999, bayan da sojoji suka mika mulki.

Mulkin karba-karba

Image caption Janar Ibrahim Badamasi Babangida

A makon da ya gabata ma tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi barazanar kauracewa jam'iyyar muddin ta bari shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takarar neman kujerar shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

Kokarin Jonathan na tsayawa takara karkashin jami'iyyar ta PDP, ya jawo cece kuce ganin cewa jam'iyyar na amfani ne da tsarin karba-karba wanda kuma ya kamata a ce arewacin kasar ne zai fidda dan takarar shugaban kasa bayan rasuwar, shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa wanda ya rasu a kan kujerar mulki a wa'adin sa na farko.

Tsohon mataimakin shugaban kasa dai Atiku Abubakar ne zai fafata da Shugaba Jonathan a zaben fidda gwani, bayan kwamitin dattawan arewa sun tsaida shi a matsayin dan takaran arewacin kasar.