Wanda ya kirkiro dandalin facebook ya zama gwarzon shekara

Mark Zuckerberg
Image caption Mark Zuckerberg

Mujallar nan ta Time, ta bayyana sunan mutumin nan da ya kirkiro shafin nan na sada zumunta na Facebook, Marck Zuckerberg, a matsayin gwarzon ta na shekara.

Babban editan Mujallar ta Time, Richard Stengel ya ce Mr Zuckerburg, ya sauya yadda jama'a suke mu'umula da juna baki daya.

Yace shafin Facebook, wanda a wannan shekarar ya samu mutane sama da miliyan dari biyar da hamsin, yana sauya hanyoyin da muke yin mu'amula da juna, da yadda muke zumunci tsakaninmu, da yadda muke magana da juna bawai kawai a Amurka ba, a'a har da sauran sassan duniya baki daya.

Wata kuri'a da aka yi a tsakanin masu karanta Mujallar ta nuna akasarinsu sun goyi bayan a baiwa mutumin nan da ya kirkiro shafin WikiLeaks, Watau Julian Assange.