Bikin samun mai a Ghana

Taswirar kasar Ghana
Image caption Yau Ghana za ta fara fitar da mai

A yau laraba ne Ghana za ta fara fitar da danyen man fetur da ta gano a yankin yammacin kasar don sayarwa a kasuwannin duniya.

Za a gudanar da bukukuwa a babban birnin jihar yammacin kasar,Takoradi mai nisan sama da kilometre dari biyu da ashirin daga birnin Accra.

Shugaba John Atta Mills ne dai zai jagoranci bukukuwan da za su samu halartar ministoci da manyan jami'an gwamnati da kuma sarakunan gargajiya.

Kimanin shekaru uku da rabi baya ne aka gano danyen man fetur a kasar, da ake kiyasin ya kai ganga biliyan guda.

Ana hasashen cinikin man zai samarwa da Ghana kimanin dala miliyan dari hudu a shekarar farko.