Ghana ta fara fitar da danyen mai a karo na farko

Kasar Ghana ta fara fitar da mai domin kaiwa kasuwannin kasashen duniya a karo na farko, bayan da kasar ta gano albarkatun danyen mai a teku, shekaru uku da suka wuce.

Shugaba John Atta Mills ne ya bude famfon bututun a wani taragon jirgin ruwa a teku.

Wata gamayyar kamfanoni da wani kamfanin Burtaniya Tullow Oil ya jagoranta ya ce yana fatan kamfanonin za su rika fitar da gangar danyen mai 55,000 a kowacce rana abin da kuma ake sa ran zai karu zuwa ganga 120,000 cikin watanni shida.

Ghana na daya daga cikin kasashen Afrika da ke zaman lafiya, kuma ana kyautata zaton za ta samu wajen dala miliyan dari hudu a shekarar farko.

Amma har yanzu dai ba'a zartar da dokar da za'a yi amfani da ita ba wajen tafiyar da sashen man kasar.

Gano danyen mai a tekun Ghana ya sa ana yi wa kasar hasashen za ta iya shiga wani hali na rashin tabbas kamar sauran kasashen Afrika da suke da danyen mai, inda ake yawan samun koma baya da kuma tashe-tashen hankula, a maimakon ci gaba.

Masana sun nuna damuwa cewa rashin zartar da dokar da za'a yi amfani da ita wajen tafiyar da sashen man kasar na iya barin baya da kura.

Gwamnati na aiki tukuru don zartar da kudurin

Gwamnatin Ghana ta yi hasashen cewa, danyen man da aka gano a kasar zai taimaka matuka wajen inganta tattalin arzikin kasar zuwa kashi biyar cikin dari a shekarar farko da kuma kashi goma sha biyu a shekara ta biyu.

Ana dai ganin fitar da man zai samar da wajen dala biliyan daya a shekara.

An yi hasashen cewa tekun farko da aka gano man wanda ake kira Jubilee Field zai samar da wajen gangar mai biliyan daya da rabi a yayinda teku na biyu da aka gano man a watan Satumbar da ta gabata zai samar da gangar mai biliyan daya da dubu dari hudu.

Wadannan wuraren da aka gano man a Ghana, su ne mafi girma da aka samu a 'yan kwanakin nan.

Daukar Darasi Daga Wasu Kasashen

Masu sa ido na ganin cewa kasar ba za ta fuskanci rikici irin na yankin Niger Delta a Najeriya ba, muddin ta aiwatar da bukatun jama'a.

"Yana da matukar mahimmacin a rika bin ka'idoji a al'umma," In Ji Stephen Hayes, Shugaban cibiyar kasuwanci ta Afrika.

"Ina ganin Ghana ta na da al'ummar da ke adalci, inda ta sha banban da wasu kasashen Afrika da ke da danyen man fetur, dama ce kasar ta samu domin yin abin da ya dace." In ji Hayes.

Ya ce za'a iya koyar darasi daga irin kurakuran da wasu kasashen Afrika suka yi, a yayinda ya ce abun da zai taimakawa Ghana shi ne, ba ta dogara da man kadai ba, saboda tana samun biliyoyin kudade wajen siyar da koko da kuma gwal.

Ya kuma ce; "Kudin shiga na siyar da mai da Ghana za ta samu kashi shida ne kacal cikin dari na kudaden shigar kasar, idan aka kwatanta da kashi 92 cikin dari na kudin shigar Najeriya, wanda tana samunsa ne daga sayar da danyen mai, sai kuma Angola wanda kashi dari na kudaden shigar ta na zuwa ne daga siyar da danyen mai."

"Wannan na nuni da cewa Ghana ba za ta dogara akan mai kadai ba, abun da kuma zai taimaka mata wajen tafiyar da tattalin arzikin kasar."

Wakilin BBC a birnin Accra, David Amanor, ya ce al'ummar kasar na cike da farin ciki kan fitar da danyen man da Ghana ta fara yi a yayinda su ke ta bada shawara kan yadda suke son gwamnatin kasar ta yi amfani da kudaden da za ta samu daga danyen man.

"Ina matukar farin ciki da wannan ci gaba da Ghana ta samu, wannan zai taimaka matuka wajen magance wasu matsalolin da kasar ke fuskanta." In ji wani dan kasuwa.

"Kamata ya yi ayi amfani da kudin wajen inganta sashen Illimi da noma da kuma kiwon lafiya"

Wani mutumin ko cewa ya yi; "Zai taimaka mun sosai, saboda na gama makaranta, amma ban samu aikin yi ba, Ina fatan zan samu aiki yi a bangaren man kasar."