Majalisar wakilai ta fusata

Harabar majalisar dokokin Najeriya
Image caption 'Yan majalisar wakilai sun fusata

Majalisar wakilan Najeriya ta fusata kan yadda takwararta ta dattawa ta yi watsi da kudirin dokar da zai baiwa 'yan majalisar damar kasancewa mambobin kwamatin zartarwar jam'iyyunsu.

Shugaban kwamitin dake sa-ido kan hukumar zabe Musa Sarkin Adar ya ce abin da majalisar dattawan ta yi yankan-baya ne ga majalisar wakilan.

Ya ce 'yan majalisar zasu gana da takwarorin nasu dake majalisar dattwan domin bayyana musu fusatar wakilan kan batun.

Ya ce:''A karon farko lokacin da muke gyaran tsarin mulki, su( 'yan majalisar dattawa),su ka kawo batun cewa ya kamata duk shugaban kwamiti( na majalisun), ya zamo dan kwamatin zartarwar jam'iyarsa.Zamu fada mu su cewa 'Menene na dawowa ku zame, ku nuna cewa kunfi mu dabara.Zamu yi Allah-wadai da su''.