Nuhu Ribadu ya kaddamar da takarar shugaban kasa

Nuhu Ribadu
Image caption Nuhu Ribadu

A Najeriya a yau ne tsohon shugaban Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati Malam Nuhu Ribadu, ya kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa.

Zai tsaya takarar ne a karkashin inuwar jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).

A jawabin da ya gabatar, Malam Nuhu Ribadu ya yi tir da yadda al'amura ke tafiya a Najeriya a halin yanzu, inda ya ce wajibi ne 'yan kasar su ta shi tsaye domin kawo sauyi.