Sojojin NATO sun kashe na Afghanistan 4

Sojojin NATO sun kashe na Afghanistan 4
Image caption An dade ana samun irin wadannan kashe-kashe a Afghanistan

Jami'ai a kasar Afghanistan sun ce wani hari da sojojin Nato suka kai ta sama ya kashe sojojin kasar Afghanistan hudu bisa kuskure.

An zaci sojojin na cikin masu tayar da kayar baya ne a lokacin da suke aikin suntiri a yankin Musa Qala na gundumar Helmand, kamar yadda jami'ai suka shaida wa BBC.

Wannan lamari ya faru ne sa'o'i kadan kafin shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar da sabon shirinsa kan kasar ta Afghanistan.

A wani lamarin daban kuma, wani bom da aka dana a gefen hanya ya kashe tare da raunata mutane da dama dake tafiya a wata karamar motar Bus a gundumar Herat.

Mai magana da yawun kungiyar tsaro ta Nato kyaftin Ciro Parisi, ya ce an tura wata tawaga domin binciken lamarin na Helmand, amma ba zai iya tabbatar da adadin rayukan da aka rasa ba.

A watan Agusta ma dai sai da aka kashe 'yan sanda uku a lokacin da sojojin Nato suka kai wani hari ta sama, yayin da a watan Yuli irin wannan hari ya kashe sojojin Afghanistan shida a yankin Ghazni.

Sai dai mai magana da yawun gwamnan Herat, Rafi Behrozan, ya shaida wa BBC cewa mutane da dama ne suka rasu lokacin da wani bom da aka dana a kan hanya ya tashi a gundumar Kushk Kuhna.