Amurka za ta kai karar kamfanin BP

Antoni Janar na Amurka, Eric Holder
Image caption Amurka za ta gurfanar da BP gaban kuliya

Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce za ta gurfanar da kamfanin mai na BP, da wasu kamfanoni takwas, wadanda ke da alhakin malalar man da ta auku a tekun Mexico a watan Afrilun bana.

Babban lauyan gwamnatin kasar, Eric Holder ya ce gwamnati ta sha alwashin gano wadanda suka yi sanadiyar jerin matsalolin da aka fuskanta a lokacin malalar man.

Ya ce kamfanin mai na BP, da takwarorinsa za su biya tara mai yawa sakamakon kasadar da su ka yi kan lamarin.

Ma'aikatar shari'ar dai ta ce ba ta san adadin barnar da malalar man ta yi ba, sai dai ta ce za a tuhumi kamfanin BP, da takwarorinsa ne da laifin haddasa mummunar malalar mai a yankin.

Wannan shari'a dai za ta sa kamfanin BP ya kashe wasu makudan kudade, baya ga wadanda ya kashe don magance malalar man a baya.