Kotu ta sake bada belin Julian Assange

Kotu ta sake bada belin Julian Assange
Image caption Mista Assange dai ya musanta zargin da ake yi masa

Wata babbar kotu a birnin London ta yi watsi da karar da jami'an Sweden suka daukaka, inda ta bada belin Julian Assange wanda ya kirkiro shafin Wikileaks mai kwarmato bayanai. Babban alkali Duncan Ouseley ya tabbatar da hukuncin da kotun farko ta bayar, inda ta bada belin Mista Assange, kafin a yanke hukunci kan batun mika shi ga kasar ta Sweden.

Ana dai neman Mista Assange ne, dan shekaru 39 a Sweden bisa zargin yi wa wasu mata fyade.

Ya dai karyata dukkan zargin, amma ya ki mika kansa ga kasar ta Sweden domin amsa tambayoyi.

A ranar Talata ne aka bashi beli kan kudi fan dubu 200, amma sai masu shigar da kara suka tafi babbar kotu suna masu cewa hakan ka iya mutumin da suke zargin ya gudu. A watan da ya gabata ne shafin Wikileaks ya fusata Amurka, bayanda ya wallafa bayanan sirrin kasar na diflomasiyya kusan dubu 250.