Ivory Coast: Tarzoma kan gidan talabijin

Zanga-zanga a Ivory Coast
Image caption Tun a lokacin zagaye na biyu na zaben ake samun tashin hankali

'Yan sanda a Ivory Coast na kokarin tarwatsa masu zanga-zangar dake goyan bayan Alassane Ouattara, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya a rikicin shugabancin da ake yi.

Suna son kaiwa ga gidan talabijin din kasar ne dake tsakiyar birnin Abidjan da niyyar kwace shi.

Sojoji masu goyan bayan shugaba Laurent Gbagbo, suna gadin ginin - sannan sun zargi masu zanga-zangar da tsokanar fada.

An ji karar fashewar wasu abubuwa da kuma harbe-harben bindiga a kewayen wurin da ake zanga-zangar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce akalla masu zanga-zangar uku ne tashin hankalin ya ritsa da su.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya nemi bangarorin biyu da su kwantar da hankali.

Mai magana da yawunsa Martin Nesirky ya gaya wa shirin BBC na Network Africa cewa :"Sakatare Janar na tunatar da masu rura wutar rikicin cewa za su girbi abinda suka shuka komai daren dade wa".

"Ya kuma maimata kiran da ya yi ga Mista Gbagbo na ya sauka daga kan karagar mulki," a cewar Mista Nesirky.