Jami'an tsaron sun bude wuta kan masu zanga-zanga a Ivory Coast

Jami'an tsaro a kasar Ivory Coast wadanda ke biyayya ga shugaban kasar Laurent Gbagbo sun bude wuta kan masu zanga-zangar dake kokarin karbar ikon gidan talabijin na kasar, inda suka halaka wasu tare da jikkata da dama.

An ji karar harbe-harbe a daukacin cibiyar kasuwancin kasar Abidjan.

Daga cikin guraren da aka ji karar harbe-harben, har da otal din da jagoran 'yan adawar kasar Alassane Ouattara ya mayar shelkwatarsa.

Tarayyar turai ta kakabawa kasar takunkumi bayanda Mr Gbabo ya ki sauka daga kan mulki, bayanda hukumar zaben kasar ta bayyana Alassane Outtara a matsayin wanda ya lashe zaben.