Rage albashin 'yan majalisar Najeriya

Harabar majalisar dokokin Najeriya
Image caption 'yan majalisa sun amince a rage albashinsu

'Yan majalisun dokokin Najeriya sun amince a rage kudaden gudanar da ayyukan yau da kullum a majalisun, koda yake ba su fadi ko da nawa suke so a rage a kasafin ba.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya ne ya bada wannan sanawar a jiya.

Honourable Sada Soli Jibia, dan majalisar wakilai ne, ya shaidawa BBC cewa sun rage kasafin kudinsu ne, saboda sun ba da umarnin rage na sauran ma'aikatun gwamnati.

Ya kara da cewa rage kudaden zai baiwa kasar damar aiwatar da ayyuka ga talakawa.

'Yan majalisar sun sha suka akan irin kudaden da ake ware musu, kama daga alawus alawus zuwa kudaden gudanar da ayyukansu na yau da kullum.