Mancini na da kwarin gwiwa kan Tavez

Tavez
Image caption An dade ana cece-kuce kan Carlos Tavez

Kocin Manchester United Roverto Mancini ya ce yana da kwarin giwar cewa Carlos Tavez zai ci gaba da zama a kulob din duk da cewa dan wasan ya nemi a barshi ya tafi.

Tavez, mai shekaru 26, ya nemi a barshi ya tafi ne a karshen mako, yana mai cewa dangantakarsa da wasu shugabannin kulob din ta yi tsamin da ba za ta gyaru ba.

Sai dai Tavez a shirye yake ya taka leda idan aka sanya shi, kamar yadda mai bashi shawara ya bayyana ranar Laraba.

"Ina so na yi magana da shi. Dan wasan mu ne, ina fatan zai ci gaba da taka mana leda da cin kwallaye kamar yadda ya saba," a cewar Mancini.

Ya kara da cewa: "Ban ji dadi ba saboda muna mataki mai kyau a yanzu a kan tebur. Carlos na da sauran shekaru uku da rabi a kwantiraginsa."