Gwamnonin PDP sun amince su goyi bayan Jonathan

Goodluck Jonathan

Gwamnonin Jam'iyyar PDP a Nigeria kamar 20 sun kuduri aniyar marawa Shugaba Goodluck Jonathan baya a zaben fidda gwani na jam'iyyar.

Gwamnonin sun bayyana haka ne bayan taron majalissar koli na Jam'iyyar da aka yi a Abuja babban birnin kasar.

A karkashin yarjejeniyar, gwamnonin sun bayyana cewar zasu marawa Shugaba Goodluck Jonathan baya ne domin ya kammala wa'adin takarar da ya fara tare da marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua.

Da ya ke bayyana matsayin gwamnonin, Gwamna Ibrahim Shehu Shema na Jihar Katsina ya ce:

"Mun zauna a matsayinmu na gwamnonin PDP, kuma an rubuta wannan jawabin bayan taro, cewa ya yarda zai sake tsayawa takara, kuma gwamnonin sun yarda za su taimaka masa".

Hakan na nufin, idan har Shugaba Goodluck Jonathan ya lashe zaben na badi, to zai yi wa'adi daya kenan akan karagar mulki.

Jam'iyyar ta PDP ta kuma amince da jaddawalin gudanar da zaben fitar da gwani. Kamar yadda jam'iyyar ta ce, za'a gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnoni gabanin a yi na shugaban kasa.

Za'a yi zaben fitar da gwanin na shugaban kasa ne a Abuja babban birnin kasar.