Julian Assange ya ce ana kokarin bata masa suna

Image caption Julian Assange

Julian Assange wanda ya kirkiro shafin Wikileaks mai kwarmato bayanai ya ce wasu ne ke kokarin bata masa suna, shi ya sa ake zargin sa da yin fyade a Sweden.

Assange wanda hukumomi a Sweden ke neman Burtaniya ta tasa keyar sa kasar ya karyata duk wani zargi da ake yi masa da ya danganci fyade. Mista Assange na zaune ne a wani gida a kusa da Bungay, Suffolk, bayan wata babbar kotu a Ingila ta bada belinsa. A ranar Talata ne aka bashi beli kan kudi fan dubu 200, amma daga bisani masu shigar da kara suka tafi babbar kotu suna masu cewa hakan ka iya sa mutumin da suke zargin ya gudu.

A watan da ya gabata ne shafin Wikileaks ya fusata Amurka, bayanda ya wallafa bayanan sirrin kasar na diflomasiyya kusan dubu 250.

Mista Assange dai ya ce shafin zai ci gaba da aikinsa na kwarmato bayanai, inda ya ce babu gudu ba ja da baya.