Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Janar Buhari ya yi tsokaci kan CPC

Image caption Janar Muhammadu Buhari ya tsaya takara a shekarar 2003 da 2007 a jam'iyyar ANPP

A kwanakin bayan ne tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Muhammadu Buhari, kuma tsohon dan takarar shugaban kasar a zaben 2003 da 2007 karkashin jam'iyyar ANPP, ya bukaci jam'iyyarsa ta CPC ta tsayar da shi a matsayin dan takarar ta a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Magoya bayan janar din dai na yi masa kallon mutum mai kwatanta gaskiya.

Amma kuma jam'iyyar janar din ta CPC na fama da rigingimu a wasu jojihin kasar, abinda ma ya sa kwamitin amintattun jam'iyyar ya soke zabubbukan cikin gida da aka gudanar a wasu jihohi sakamakon magudin da kwamitin ya ce an tafka.

Idan jamiyyar CPC ta tsayar da janar din a matsayin dan takarar ta a zaben shugaban kasa mai zuwa, to karo na uku kenan a jere da janar Muhammadu Buharin zai yi takarar shugaban kasar.

A filinmu na Gane Mani Hanya, Jimeh Saleh ya tattauna da Janar Muhammadi Buhari.

Kuma ya fara ne tambayarsa: Ko me ya sa ba zai hakura ba tunda ya yi takara har sau biyu a baya ba tare da nasara ba?