Kalaman Atiku: 'Cin amanar kasa ne' - Jonathan

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya, yayinda zabubbukan kasar na shekarar 2011 ke karatowa, wasu alamu na nuna zafafar yakin neman zabe tsakanin manyan 'yan takarar dake neman shugabancin kasar karkashin inuwar jam'iyar PDP.

Shugaban kasar Goodluck Jonathan a wani jawabi mai kama da hannunka mai sanda ya bayyana furucin da tsohon mataimakin shugaban kasar yayi na cewa duk wadanda ke kokarin hana tabbatar da samun sauyi cikin ruwan sanyi, to su kwan da sanin cewa za'a iya samar da shi ta hanyar tashin hankali, da cewa tamkar cin amanar kasa ne.

Sai dai a martanin da ya mayar, Alhaji atiku Abubakar ya ce kazafi ne kawai aka yi masa da nufin a bata masa suna.

Yanzu dai a bayyana take cewa, yakin neman zaben kujerar shugaban kasar tsakanin manyan 'yan takara biyu a jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya na kara zafafa, inda ake ci gaba da cacar baki tsakanin bangaren shugaba Goodluck Jonathan da bangaren tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.

Musayar kalamai

Musayar kalamai na baya bayan nan dai shi ne furucin da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar yayi na cewa duk wadanda ke kokarin hana tabbatar da samun canji cikin ruwan sanyi, to kuwa su kwan da sanin cewa za'a iya samar da shi ta karfi da yaji.

Alhaji Abubakar Mu'azu, darakta a kungiyar yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan ya shaidawa BBC cewa, ko kadan, basu ji dadin wadannan kalamai ba.

Image caption Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar

"Gaskiya ba mu ji dadin maganar da Atiku ya yi ba, domin bamu da wurin zuwa da ya wuce Najeriya, tashin hankali ba shi da amfani. Irin wadanan kiraye-kirayen shi ke tunzura talaka." In ji Alhaji Abubakar Mu'azu. To sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar yayi watsi da hannunka mai sanda da shugaban kasar yayi na cewa irin wadannan kalamai tamkar cin amanar kasa ne.

"Babu wani maganar cin amanar kasa. Wannan magana ce ta siyasa, ina ganin Shugaban kasa ya firgita ne. Abin da na fada, wani jawabin shugaban Amurka ne na maimata, kuma ba wai ina fatan hakan ya faru a Najeriya ba ne." In ji Atiku Abubakar.

Abin da yanzu 'yan siyasa da wasu 'yan kasar da dama ke jira su gani dai shi ne yadda zabbukan fidda gwani na jam'iyar za su kasance, abin da masu iya magana ke cewa ba a san maci tuwo ba