Ivory Coast: Kwamitin Sulhu ya yi gargadi

'Yan sandan Ivory Coast sun tunkari magoya bayan Alassane Ouattara
Image caption 'Yan sandan Ivory Coast sun tunkari magoya bayan Alassane Ouattara

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa za a hukunta duk wanda aka samu daga bangarorin kasar Ivory Coast biyu da laifin kai hari a kan fararen hula kamar yadda dokokin kasa-da-kasa suka tanada.

Kwamitin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a daidai lokacin da aka samu labarin arangama a kasar.

Sanarwar ta Kwamitin Sulhun ta nuna matukar damuwa game da tashe-tashen hankulan da ake yi a kasar ta Ivory Coast.

Kwamitin Sulhun dai, da ma sauran hukumomin kasa-da-kasa, sun amince da jagoran 'yan adawa, Alassane Ouattara, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Sai dai abokin adawarsa kuma shugaban kasa mai ci, Laurent Gbagbo, ya yi kememe ya ki amsa kiran da ake yi masa na ya sauka daga mukamin nasa.

Sojoji masu biyayya ga shugabannin kasar biyu dai sun yi musayar wuta lokacin da magoya bayan Mista Ouattara suka yi yunkurin maci zuwa hedkwatar gidan talabijin mallakar gwamnatin kasar.

An kuma yi musayar wuta a wani gari da ke tsakiyar kasar.

Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya ya ce an kara yawan sojojin da ke samar da tsaro a otal din da Mista Ouattara ya ke zuwa dari takwas, yayinda rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar ta ke tuntubar bangarorin biyu don kwantar da hankula.

An dai bayar da rahoton cewa akalla mutane ashirin ne suka rasa rayukansu bayanda magoya bayan shugabannin kasar biyu suka yi fito-na-fito.

Karin bayani