Japan ta sauya manufofinta na tsaro

Sojojin kasar Japan
Image caption Sojojin kasar Japan

A wani sabon nazari da ta gudanar a kan manufofin tsaronta, Japan ta bayyana karin karfin rundunar sojin China da cewa abin damuwa ne ga kasashen duniya.

Kundin sababbin manufofin tsaron da Majalisar Ministocin Japan din ta amince da shi ne dai zai shatawa kasar ta Japan manufofin tsaronta a shekaru goma masu zuwa.

Kasar ta Japan ta sauya manufofinta na tsaro ne domin su dace da sauye-sauyen da ake samu ta fuskar tsaro a nahiyar Asiya.

Kasar ta ce za ta kara yawan dakarunta a tsaunukan da ke kudanci, kusa da China.

Za kuma a rage matakan tsaron da aka girke a arewacin kasar tun lokacin yakin cacar baka da nufin dakile duk wani yunkurin mamaya daga Rasha.

Za a rage yawan tankokin yaki da kashi daya bisa uku, yayinda za a kara yawan jiragen ruwan yaki na karkashin ruwa a kuma inganta jiragen saman yaki.

Kundin manufofin tsaron ya kuma bayyana cewa makaman Korea ta Arewa masu linzami da ma makamanta na nukiliya ka iya kawo yamutsi.

Don haka ne za a kara yawan makaman ba da kariya daga harin makamai masu linzami a fadin kasar ta Japan.

Japan dai ta fi Birtaniya yawan sojoji, to amma kundin tsarin mulkin kasar ya haramta musu fara kai farmaki.

Kasashen nahiyar Asiya, wadanda har yanzu ba su manta da cin zalin da Japan ta aikata lokacin yakin Duniya na Biyu ba, za su sa ido sosai a kan wadannan sababbin manufofin tsaro na kasar ta Japan.