An yankewa mutane 17 hukunci a kan rikicin Jos

Rikicin Jihar Plateau

Wata babbar kotun tarayya a Jos, babban birnin jihar Plateau, ta yankewa wasu mutane hukuncin dauri a gidan kaso, bayan ta same su da hannu a tashe-tashen hankula a jihar.

Kotun, a karkashin mai shari'a Ambrose Allagoa, ta sami mutanen da laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, da kuma ta'addanci.

Rahotanni sun ce an yankewa jumlar mutane goma sha bakwai hukunci a wasu zama guda biyu da kotun ta yi ranar Alhamis da kuma Juma'a.

An tuhumi mutanen ne da laifin samun hannu a kashe kashen kabilancin da aka yi a garin Dogo na Hauwa, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa.

An kama mutane, wadanda dukkaninsu fulani ne makiyaya, bayan wani tashin hankali tsakanin kiristoci manoma da makiyaya da aka yi a cikin watan Janairu na wannan shekarar.

Lauyan wadanda aka yankewa hukuncin ya ce zasu daukaka kara.