Saraki ya ce banda shi a goyan bayan Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya, Gwamnan jihar Kwara, Dr Bukola Saraki, ya nisanta kansa daga matsayin da wasu takwarorinsa na PDP suka dauka, na goyon bayan takarar shugaba Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana cewa bai goyi bayan tafiyar ba ne, saboda yunkurin shugaban kasar, wani take-take ne na sabawa tsohuwar yarjejeniyar da `ya`yan jamaiyyar suka kulla, ta tsarin mulkin kar-ba-karba.

A jiya ne dai wasu gwamnoni 20 na jam'iyyar PDP suka fitar da shelar cewa za su goyi bayan shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben fitar da gwani na Jam'iyyar PDP.

Sanarwar ta kara da cewa zasu goyi bayan Jonathan ne domin ya kammala takarar da ya fara a karkashin tikitin da aka baiwa marigayi Umaru Musa 'Yar'adua.

An cimma wannan yarjjeneya ce bayan da gwamnonin suka ki amincewa a sauya tsarin zaben fitar da gwani na Jam'iyyar. A karkashin tsarin na yanzu sai an kammala zaben fitar da gwani na gwamnoni gabanin a yi na shugaban kasa.

Jam'iyyar ta PDP ta ce zata yi zaben fitar da gwani na shugaban kasa ranar 13 ga watan Janairu.