Nijar ta cika shekaru 52 da zama jamhuriya

Shugaban mulkin sojan Nijar, Salou Djibo
Image caption Shugaban mulkin sojan Nijar, Salou Djibo

A Jamhuriyar Nijar, yau ne ake shagulgulan bikin cika shekaru hamsin da biyu da zaman kasar jamhuriya.

A ranar 18 ga watan Disamban 1958 ne dai kasar ta Nijar ta zama jamhuriya.

Don murnar wannan rana ne kuma shugaban mulkin sojan kasar, Janar Salou Djibo, ya yi wani jawabi inda ya yi kira ga 'yan kasar da su karfafa hadin kai a tsakaninsu, sannan su bayar da hadin kai da goyon baya ga shirin girka hukumomin jamhuriya ta bakwai.

A cewar Janar Salou Djibo: “An ga abubuwa na ci gaba, an kuma ga abubuwa na koma-baya: daga 1960 zuwa 2010 jamhuriya shida ‘yan Nijar suka gani.

“Hakan kuma na nuna cewa har yanzu da sauranmu”.

Shugaban mulkin sojan ya kuma yi kira ga ’yan Nijar su yi aiki tukuru su kuma guji dogaro a kan wani mutum wanda zai zamo shi ne ci, shi ne sha, shi ne wurin kwana—wannan, a cewarsa, ba ya haifar da alheri ga kasa.