Richardson ya yi gargadi dangane da Korea

Sojojin Korea ta Kudu
Image caption Sojojin Korea ta Kudu suna sintiri a tsibirin Yeonpyeong

Kwararren mai shiga tsakani ta fuskar diflomasiyya, Bill Richardson, wanda ke ziyarar da ba ta aiki ba a Pyongyang, ya bayyana dangantaka tsakanin kasashen Korea ta Arewa da ta Kudu da cewa wata nakiya ce da ka iya tashi ko wanne lokaci.

Mai shiga tsakanin, wanda kuma shi ne gwamnan Jihar New Mexico da ke Amurka, ya ce ya bukaci jami'an Korea ta Arewa su yi taka-tsantsan kuma ya yi amannar ba-da-bakin nasa ya dan yi tasiri.

Ya kuma ce yana jin hukumomin kasar ta Korea ta Arewa suna kokarin ganin sun dan sassauta matsayinsu.

Akwai fargabar al'amura za su kara rincabewa a dangantakar da ke tsakanin kasashen na Korea sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan harin da Korea ta Arewa ta kai kan tsibirin Yeonpyeong wanda ake takaddama a kan shi.

Har yanzu dai ana zaman dar-dar yayinda Korea ta Kudu ta ke shirin kaddamar da wani atisaye daura da tsibirin, wanda ke kusa da iyakokin kasashen biyu.

Kafofin yada labarai na Korea ta Arewa sun yi gargadin cewa in har aka kaddamar da atisayen, kasar za ta kai hare-haren da suka fi na baya muni.

To amma Mista Richardson ya ce ga alamu Korea ta Arewan ta sauya shawara.