Obama ya nemi amincewar Majalisar Dattawan Amurka

Shuagaba Obama
Image caption Obama ya ce wannan yarjejeniya na da mahimmanci sosai

Shugaban Amurka Barrack Obama ya ce duk wata gazawa daga bangaren 'yan Majalisar Dattawan kasar na kin amincewa da sabuwar yarjejeniyar makamai da kasar Rasha, ka iya yin illa ga shugabancin Amurka.

A jawabinsa na mako-mako ta gidan rediyo, Mr. Obama ya bayyana cewa kin rattaba a hannu a yarjejeniyar da akewa lakabi da suna "New START", ka iya maida hannun agogo baya dangane da ci gaban da Amurka ta samu ta fuskar dangantakarta da kasar Rasha.

Ya kuma kara da cewa matukar babu sabuwar yarjejeniya, hakan ka iya kawo cikas ga ci gaban da Amurka ta samu a dangantakar ta da Rasha.

Kasar Amurka dai ta ce yarjejeniyar na da matukar muhimmanci wajen sanyawa kasar Iran takunkumi mai tsauri, tare kuma da kwato duk wasu na'urorin harhada makaman nukiliya daga hannun 'yan ta'adda.