Sojan Afghanistan sun hallaka a hare hare

Hari a Kabul
Image caption Hari a Kabul

'Yan kunar bakin wake sun hallaka dakarun Afghanistan akalla 13, a wasu hare hare biyu da suka kai a babban sansanin horar da sojan Afghanistan din a birnin Kabul, da kuma a wata cibiyar daukar ma'aikatan soja da ke birnin Kunduz na arewacin kasar.

Biyar daga cikin maharan sun mutu.

Sojojin kawance da na Afghanistan sun yi wa cibiyar daukar ma'aikatan sojan da ke Kunduz kawanya.

Ana jin cewa, an rutsa da kimanin mutane dari a cikin ginin.

A ranar Asabar, Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ziyarci dakarun Jamus da ke Kunduz.