Arewacin Sudan zai jaddada shari'ar Musulunci

Shugaban Sudan, Omar al-Bashir
Image caption Shugaban Sudan, Omar al-Bashir

Shugaban Sudan, Omar al-Bashir, yace yankin arewacin kasar zai karfafa dokokin shari'ar Musulunci, idan kudancin kasar ya kada kuri'ar ballewa, a lokaci zaben raba gardamar da za a yi a watan Janairu mai zuwa.

Lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a garin Gedarif, Mr Bashir yace za a sauya kundin tsarin mulkin kasar idan kasar ta dare gida biyu: Larabci zai kasance shine harshe daya tilo a kasar, Musulunci kuma addini daya da aka amince da shi, sannan za a yi aiki da shari'ar Musulunci kawai a kasar.

Wakilin BBC a birnin Khartoum ya ce, ko shakka babu kalaman shugaba al-Bashir zasu janyo damuwa a zukatan dimbin 'yan kudancin Sudan, wadanda ba Musulmi ba, wadanda ke zaune a arewacin kasar.

Wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka amince da ita a shekara ta 2005, wadda ta kawo karshen yakin basasar kasar, ta takaita aiki da shari'ar Musulunci a arewacin Sudan.