'Tattalin arzikin Cuba na cikin hadari'

Shugaba Raul Castro na Cuba
Image caption Shugaba Raul Castro na Cuba

Shugaban kasar Cuba, Raul Castro, ya bukaci mutanen kasar su goyi bayan shirin da yake yi na aiwatar da wadansu sauye-sauye ga tsarin tattalin arzikin kasar.

A wani dogon jawabi da ya yiwa majalisar dokokin kasar, Shugaba Castro ya ce sauye-sauyen, wadanda za su saukaka kayyade-kayyaden da aka sanyawa 'yan kasuwa masu zaman kansu, an tsarasu ne domin su ceto tsarin gurguzu, ba don a dawo da tsarin jari hujja ba.

Ya ce kasar Cuba tana cikin hadari har sai an warware matsalolinta na tattalin arziki.

Jam'iyyar Kwaminisancin kasar Cuban dai za ta gana a watan Afrilu domin amincewa da sauye-sauyen a hukumance, wadanda suka hada da shirin rage ma'aikatan kasar zuwa kusan mutum dubu dari biyar.